A yau Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ta shigar na neman a yi gyara kan wasu tanade-tanade da ke cikin dokokin ‘yan sandan Najeriya.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a cikin hukuncin da ya yanke, ya ce babu wani abu na nuna wariya ko kuma ya sabawa doka game da tanade-tanaden da ke cikin dokoki 126 da 127 na NPR.
Mai shari’a Ekwo ya yanke hukuncin cewa duk wadda ta shiga aikin ‘yan sanda, ta san da ka’idojin, don haka ba daidai ba ne wata ‘yar sanda ta ce za ta karya wannan ka’ida.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa NBA ta bayar da hujjar cewa dokokin 126 da 127 na NPR, sun ci karo da sashe na 37 da 42 na kundin tsarin mulkin kasar.
Kuma doka ta 127 ta tanadi cewa ‘’yar sandan da ba ta yi aure ba, wadda ta dauki ciki, za a sallame ta daga aiki kuma ba za a sake shigar da ita ba sai da izinin babban sufeton ‘yan sanda.
Sai dai sashe na 37 na kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa kowane dan Najeriya yancin zaman kansa da na iyali, yayin da sashe na 42 ya tanadi ‘yancin walwala daga wariya.
Hukumar ta NBA ta bayar da hujjar cewa duka tanade-tanaden da ke cikin NPR ba wai kawai nuna wariya ga jami’an ‘yan sanda mata da ba su yi aure ba, har ma sun mayar da da dama daga cikin ‘ya’ya saboda tsoron a kore su daga aiki.













































