Daraktan cibiyar ICICE da masallacin Al-Noor Abuja Kabir Kabo Usman ya rasu

WhatsApp Image 2025 12 21 at 11.02.32 706x430

Daraktan cibiyar al’adu da ilimin addinin musulunci ta duniya wato International Centre for Islamic Culture and Education da ke kula da Masallacin Al-Noor a Wuse 2 a Abuja, Dr. Kabir Kabo Usman, ya rasu.

Makusancin marigayin, Kwamared Abdulkadir Ahmed Ibrahim, ya tabbatar wa jaridar Solacebase cewa Dr. Kabir Usman ya rasu a ranar Asabar a wani asibiti da ke birnin Manchester na ƙasar Birtaniya bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Iyalan marigayin sun bayyana cewa za a sanar da lokacin jana’izar a nan gaba.

Dr. Kabir Kabo Usman ya kasance fitaccen malamin addinin musulunci, shugaba a fannin gudanarwa kuma ma’aikacin gwamnati, wanda ya shahara wajen bayar da gudummawa a ilimin addini, gyaran bangaren gwamnati da bunƙasa ƙwarewar ɗan Adam a Najeriya da ma ƙasashen waje.

Kafin nadinsa a cibiyar ICICE, ya taɓa zama Darakta Janar na cibiyar bunƙasa gudanarwa wato Centre for Management Development daga shekarar 2010 zuwa 2018, wata hukuma da ke ƙarƙashin tsohuwar ma’aikatar tsare-tsaren ƙasa, inda ya taka rawa wajen ƙarfafa tsarin gina ƙwarewa da inganta ƙa’idojin gudanarwa a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu.

An haifi Dr. Kabir Usman a garin Kabo da ke ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano, yana da shekaru 67 a lokacin rasuwarsa.

Ya fara karatunsa a makarantar firamare ta Kabo, sannan ya yi sakandare a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Dambatta, inda ya kammala a shekarar 1975.

Daga nan ya tafi jami’ar Bayero da ke Kano inda ya samu digiri na farko a fannin sinadarai, kafin daga bisani ya yi digirin digirgir da na gaba-gaba a jami’ar Manchester da ke ƙasar Birtaniya.

A lokacin da yake can, ya yi aiki a jami’ar Manchester na kusan shekaru ashirin, yana koyarwa, bincike da horas da ɗalibai.

An yi addu’o’i na neman rahamar Allah ga marigayin, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here