Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa da shi ta ƙasa ICPC ta gayyaci attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote da ya bayyana a gaban kwamitin bincikenta a ranar Litinin a birnin Abuja, dangane da ƙorafin da shi kansa ya shigar.
Aliko Dangote ya shigar da ƙorafi kan Ahmed Farouk, tsohon darakta janar na Hukumar kula da harkokin mai da kayyade farashi ta ƙasa bisa zargin cin hanci da almundahana.
Wata majiyar kusa da hukumar ya tabbatar da cewa an kafa kwamitin ƙwararrun masu bincike domin gudanar da binciken, tare da umarnin shugaban hukumar, Dr. Musa Aliyu, SAN, da ya mayar da hankali kan ƙorafin da Dangote ya shigar.
Ana sa ran Aliko Dangote zai bayyana da kansa ko kuma ya turo lauyansa, Ogwu Onoja, SAN, tare da dukkan hujjojin da ke goyon bayan ƙorafin, yayin da binciken hukumar ya fara a hukumance.
Labari mai alaƙa: ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafin Dangote kan shugaban hukumar NMDPRA, ta ce za a bincika ƙorafin yadda ya dace
Ƙorafin ya nuna cewa Ahmed Farouk ya aikata cin hanci da amfani da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da kashe miliyoyin daloli wajen karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu masu tsada a ƙasar Switzerland, ba tare da hujjar halalcin kuɗin ba.
Haka kuma ƙorafin ya zargi Farouk da rage bunƙasar tace man fetur a cikin gida ta hanyar haɗa baki da ’yan kasuwar ƙetare da masu shigo da man fetur, ta ci gaba da bayar da lasisin shigo da mai daga waje.
Ko da yake Farouk ya yi murabus daga mukaminsa, hukumar ta jaddada cewa binciken zai ci gaba ba tare da la’akari da murabus ɗin ba.
Hukumar ta kuma tabbatar da karɓar ƙorafin a ranar 16 ga watan Disamba ta hannun lauyan Dangote, tare da bayyana cewa za a gudanar da bincike cikin adalci ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.
NAN













































