Kungiyoyin farar hula sun yi Allah wadai da matakin da matakin gwamnatin Kano na sanya ido kan kungiyoyi masu zaman kansu

Abba Kabir Yusuf 595x430

Ƙungiyoyin sa kai sun yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka a baya-bayan nan na kafa wani kwamiti da zai rika sanya ido kan ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu a jihar, inda suka bayyana matakin a matsayin mai tsauri kuma saba wa kundin tsarin mulki.

A ranar alhamis, wasu mashahuran kungiyoyin 18 sun rattaba hannu kan wata sanarwa da ke nuna matukar damuwarsu game da babban aikin kwamitin da aka kafa da kuma barazanar da suke ganin zai haifar ga ‘yancin cin gashin kan jama’a.

Sun yi iƙirarin cewa shirin wani yunƙuri ne na murkushe muryoyin kungiyoyi masu zaman kansu da sarrafa yancin jama’a.

Kungiyoyin sun yi fargabar cewa kwamitin, tare da ikonsa da kuma jagoranci mai cike da shakku, yana neman kwantar da muryoyin su da kuma lalata yunƙurin bayar da shawarwari.

SolaceBase ta bayar da rahoton cewa ayyukan kwamitin sun hada da bayyana kungiyoyi masu zaman kansu, binciken hanyoyin samar da kudade, tantance hanyoyin aiki, ba da shawarar tsarin gudanarwa, har ma da rufe ofisoshin kungiyoyi masu zaman kansu idan sun saba doka.

Kungiyoyin fararen hular sun yi gargadin cewa irin wannan iko zai iya haifar da murkushe kungiyoyin da ke aiki a sassa masu mahimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, da yancin ɗan adam.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai sanya ido kan ayyukan kungiyoyi

Bugu da kari, sun bayyana rashin sanin dalilin da ya sa gwamnati ta samar da wannan shiri, wanda aka tsara shi a matsayin daidaita ayyukan kungiyoyin sa kai da manufofin jihar.

Haka kuma sun yi kamanceceniya da wani yunkuri makamancin haka a matakin tarayya a shekarar 2017, wanda aka yi watsi da shi saboda yawan adawa.

Sun bada misalin cewa dokokin da ake da su, ciki har da Dokar Kamfanoni ta Allied Matters Act (CAMA) 2020 da dokar hadin gwiwa da gwamnati (OGP), sun riga sun ba da isasshen kulawa ga kungiyoyi masu zaman kansu.

A cewar kungiyoyin, wani muhimmin abin da ake ta cece-kuce a kai shi ne nadin Ibrahim Abdullahi Waiya, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, a matsayin shugaban kwamitin.

Kungiyoyin sun nuna damuwarsu kan shugabancin da ya yi a baya na kungiyar farar hula ta Kano (KCSF), wanda ke tattare da cece-kuce, da rashin kudi, da kuma kararrakin da kwamitin amintattu na kungiyar ke yi.

Sun bayyana cewa Waiya a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na KCSF ya fuskanci rashin da’a da kuma karkatar da kudade, sun kara da cewa kin bayar da asusu na kudi ko fitar da wasu muhimman takardu ya haifar da babbar tambaya game da cancantar sa na kula da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu.

Kungiyoyin farar hula na kira da a gaggauta rusa kwamitin, tare da yin kira ga gwamnatin jihar Kano da ta rusa shi, tare da dakatar da duk wasu ayyukan da suka shafi kungiyoyi masu zaman kansu.

Sun kuma bukaci gwamnati ta fito fili ta tabbatar da aniyar ta na tabbatar da ‘yancin cin gashin kan jama’a da samar da yanayin gudanar da ayyukansu, tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gudanar da mulki, da kaucewa nade-naden mukamai da ka iya kawo cikas ga amincewar jama’a, da kuma shiga tattaunawa da kungiyoyi masu zaman kansu maimakon yanke hukunci kai tsaye.

Sun kuma dage kan cewa dole ne gwamnati ta mutunta ‘yancin walwala da fadin albarkacin baki da tsarin mulki ya ba su.

Sanarwar ta karkare da kudurin wayar da kan al’umma, da yin shawarwari, da hada kai da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa domin kare martabar al’umma a jihar Kano.

Kungiyoyin farar hula da suka rattaba hannu kan sanarwar sun hada da (CISLAC), (CITAD), (CHRIceD), (IWEI), (WOFAN), (AHIP), (AHIP), (UAD) Kano, (YEDA).

Sauran sun hada da (CEFSAN), (AFRI-CIRD), (BCAI), (CS-CRIN), da kungiyar fafutukar kwato hakkin yara da wayar da kai ta ƙasa, da cibiyar fafutukar kwato hakkin dan Adam da wayar da kai ta ƙasa da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here