Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka (ICPC) ta yi karar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon Babban Mai Ba shi Shawara na Musamman, Jimi Lawal da wasu karin mutum 5 kan sabuwar tuhuma mai dauke da kara 11 kan zargin cin hanci, halasta kudin haramun da sauran laifuka masu alaka da su.
An shigar da wannan sabuwar karar mai lamba FHC/KD/93C/2026 a gaban Mai Shari’a Hauwa’u Buhari ta Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna. Mallam Nasir Ahmad El-Rufai shine wanda ake tuhuma na 1 tare da Jimi Adebisi Lawal, Singularity Network Security Limited, Solar Life Nigeria Limited, Knowledge Investment Nigeria Limited, Intercellular Nigeria Limited da Noble Coast Resources Limited.
A cewar karar, hukumar ta zargi Mallam El-Rufai da cewa yayin da yake Gwamnan Jihar Kaduna, ya amince da ba da kwangilar saye, tsara, shirin karshe da shigar da tsarin kyamarori na CCTV ba bisa ka’ida ba a Birnin Kaduna kan kudi N8,682,574,054.94 ga Singularity Network Security Limited, duk da cewa kamfani ne da ake zargi ba shi da kwarewa da cancantar da ake bukata, haka nan ya saba wa dokokin sayayyar gwamnati.
Hukumar ta kara zargin cewa an canza kudin da aka samu daga wannan aiki ba bisa ka’ida ba ta hannun kamfanoni da mutane daban-daban.
Sabuwar karar ta kunshi tuhume-tuhume da dama da suka shafi zargin mallaka, karba da jigilar kudi da ake zargi samfura ne na ayyukan da ba bisa ka’ida ba, inda kudin ya kai biliyoyin naira.
Mallam El-Rufai da Lawal duka sun musanta laifin lokacin da aka karanta musu tuhumar.
Sai aka dage shari’ar zuwa ranar 1 ga Yuli 2026, domin yanke hukunci kan bukatar beli, kamar yadda sanarwar da J. Okor Odey, babban jami’in yada labarai da sadarwa na hukumar ya sanya wa hannu ya bayyana wa ’yan jarida a ranar Alhamis.













































