Dakataccen shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Ondo ya rasu

Jihar ondo, shugaban, jam'iyya, PDP, rasu
Dakataccen shugaban jam'iyyar PDP a Jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu kwanaki 43 bayan dakatar da shi daga jam’iyyar. Fatai Adams, ya rasu ne sakamakon ciwon...

Dakataccen shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu kwanaki 43 bayan dakatar da shi daga jam’iyyar.

Fatai Adams, ya rasu ne sakamakon ciwon kai a gidansa da ke Ikare Akoko a daren Talata.

Kwamitin gudanarwar PDP na jihar sun dakatar da Adams ne a ranar 2 ga watan Janairun 2024 saboda zargin zagon kasa ga jam’iyyar.

Karanta wannan: ’Yan sanda sun kama rikakkun ’yan bindiga tare da kwato kudin fansa a Abuja

An kuma zarge shi da yin wasu abubuwa da ka iya janyo wa jam’iyyar adawar abin kunya.

Dakatarwar ce ta ba da damar zaman Mista Tola Alabere shugaban riko.

Wata majiya ta bayyana cewa har ila yau sun kasa samun kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Kennedy Peretie domin jin ta bakinsa kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here