2027: Gwamna Yusuf ya nemi goyon bayan sake zaben Tinubu

729364290 4509300625981824 1837679521063201227 n 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga al-ummar jihar da su cigaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugaban ya cancanci samun goyon baya mai yawa daga jama’a saboda jajircewarsa wajen bunkasa jihar da kasar baki daya.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.

Gwamna Yusuf ya yi kiran ne a Fadar Gwamnati da ke Kano, yayin da yake miƙa Takardar Shaida cin zabe ga sabon dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, Hon. Shu’aibu Rabi’u Nagogo Abba Gano.

Gwamnan ya ce mutanen Kano suna da duk wani dalili da zai sa su tsaya tsayin daka a bayan Shugaba Tinubu gabanin zaben gama-gari na 2027.

Ya bayyana cewa dangantaka da jituwar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da haifar da sakamako mai kyau ga jihar.

Gwamna Yusuf ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa tallafawa manyan ayyukan more rayuwa da ci gaba a fadin Kano, in da ya bayyana shi a matsayin shugaban da ya himmatu wajen hadin kan kasa da ci gaba.

Ya roki shugabannin siyasa, masu ruwa da tsaki da magoya baya a fadin jihar da su kasance cikin hadin kai su kuma yi aiki wajen karfafa hadin kai tsakanin jihar da Gwamnatin Tarayya.

Gwamnan ya kuma taya Hon. Shu’aibu Rabi’u Nagogo murna bisa nasararsa a zaben, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa cewa zai wakilci mutanen Dawakin Kudu da Warawa yadda ya kamata a Majalisar.

Gwamna Yusuf ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen gaba da manufofi da shirye-shiryen da ke nufin inganta rayuwar ’yan kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here