Tsohuwar Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta ziyarci tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.
Atiku ya bayyana ziyarar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, inda ya bayyana ganawar da tsohuwar Uwargidan Shugaban Kasar a matsayin babba kuma mai zurfi matuka.
Read also: Barazanar Ambaliya: NEMA ta gana da gwamnonin jihohin kasar nan
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce ziyarar ta kuma jaddada bukatar masu neman kyakkyawar Najeriya da su ba da fifiko ga walwala da makomar ‘yan Najeriya.
“A yau, na yi farin cikin karbar tsohuwar Uwargidan Shugaban Kasa, H.E. Aisha Buhari. Ziyararta ta kasance babba kuma mai zurfi matuka.”
Ya ce iyalai a fadin kasar na fuskantar matsin lamba sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da sauran abubuwa masu mahimmanci, ciki har da abinci, sufuri, ilimi da lafiya.
Ya kara da cewa, “Baya ga alhakin wannan lokaci, hakan kuma tunatarwa ce ta gaggawar alhakin da ke kan duk wanda ke neman kyakkyawar Najeriya a sanya walwala, mutunci da makomar jama’armu a gaba.”
Read also: Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunayen ministoci
Atiku ya ce ‘yan Najeriya sun cancanci tattalin arzikin da zai samar da damammaki da bai wa iyalai damar rayuwa cikin mutunci da bege.
“A fadin kasarmu, iyalai na cikin matsi sakamakon hauhawar farashin abinci, sufuri, ilimi, lafiya da sauran abubuwan more rayuwa. ‘Yan Najeriya sun cancanci tattalin arzikin da ke ba da sakamako ga aiki tukuru, dawo da samun dama da bai wa kowane iyali damar rayuwa cikin mutunci da bege.”
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce gina irin wannan kasa zai bukaci kokarin hadin gwiwa don rage wa ‘yan Najeriya nauyi da dawo da bege.
“Wannan ita ce Najeriya da ya zama wajibi mu gina tare, kasar da ke aiki ga al’ummarta. Wajibi ne mu rage nauyi, mu dawo da bege mu kuma dawo da Najeriya mai sauki.”
Read also: Cikin hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya ziyarci Jihar Plateau
Ko da yake a cikin Atiku ko Aisha babu wanda bayyana manufar ziyarar ko bayanan tattaunawarsu ba, ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara zafi gabanin babban zaben 2027.
Aisha na tare da daya daga cikin ‘ya’yanta mata da wasu abokanta yayin ziyarar.












































