Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya ki amincewa da alkaluman jinkirin jiragen da ke kunshe a rahoton hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa (NCAA) na watan Agusta ba, inda ya ce bai nuna yawan jigilar jiragen da kamfanin ya yi ba.
Kamfanin ya bayyana cewa rahoton bai kuma sanya a muhimman abubuwan da suka haddasa jinkirin da aka samu a watan ba.
Read also: Zargin ɓatanci: Sheikh Lawan Triumph ya bayyana a gaban Majalisar Shura ta Jihar Kano
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babbar Jami’ar Gudanarwa ta kamfanin, Mrs Oluwatoyin Olajide, ta sanya wa hannu a ranar Alhamis a Legas.
Idan za a iya tunawa NCAA, a cikin rahoton, ta nuna cewa Air Peace ya yi jinkiri na sama da 1330 daga cikin 1864 da ya yi a watan ya kuma soke bakwai.
Sai dai Olajide ta ce kamfanin ya gudanar da jigila sama 2,564 a watan Agusta, sabanin jiragen sama 1,864 da ke kunshe cikin rahoton NCAA.
A cewarta, bambancin da ya wuce jiragen sama 700 ya shafi lissafin yawan jinkirin da aka ruwaito.
Kamfanin jirgin saman ya kuma yi tambaya kan rashin kwatanta bayanan watan Agusta da na watan Yuli, inda ya bayyana cewa an fitar da rahoton NCAA na Agusta kwanaki kadan bayan watan ya kare.
Read also: Somaliya ta amince da yarjejeniyar tsaro da Turkiyya
Air Peace ya ce ya kamata a yi la’akari da alkaluman watan Agusta da kuma cikas din da aka samu sakamakon yajin aikin da kungiyoyin sufurin jiragen sama suka yi a ranar 11 ga Agusta.
Ya ce cikas din ya shafi ayyukansa na tsawon kwanaki sama da 14, wanda ya haifar da sauya jadawalin jigilar jiragen, tare da soke wasu jigilolin.
Ya kara da cewa rahoton NCAA bai rarrabe sosai tsakanin jinkirin da ya samo asali daga abubuwan da suka shafi ayyukan cikin gida da wadanda ke faruwa sakamakon yanayi na waje ba.
Olajide ta ce binciken da suka yi a ciki ya nuna cewa jigila 391, wanda ke wakiltar kusan kashi 15 cikin 100 na jinkirin da aka samu a cikin watan, ya faruwa ne sakamakon abubuwan da suka shafi cikin gida.
Ta gano matsalolin fasaha da ke bukatar gyaran jirgi da ba a tsara ba da kuma al’amuran da suka shafi man fetur a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da matsalar cikin gida.
Ta ce abubuwan da suka shafi waje sun hada da cunkoson filin jirgin sama da kalubalen hanyoyi, karo da tsuntsaye, munanan yanayi, yajin aiki da kuma lalacewar jirgin sama daga kamfanin kula da filin jirgin.
Read also: Wasu kwamishinonin biyu sun yi murabus daga majalisar zartarwar Fubara
Olajide ta ce cunkoson filin jirgin sama da zirga-zirga sun kai sama da kashi 51 cikin 100 na jinkirin da aka samu daga waje, inda ake tsare jiragen a kasa a wasu lokutan ko kuma a rike su saboda karancin karfin filin jirgin.
Ta kuma ambaci karo da tsuntsaye a matsayin wani abin da ya shafi ayyukanta.












































