Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya isa Jos, babban birnin jihar Filato, a ziyarar jaje ga gwamnati da al’ummar jihar.
Ziyarar ta san a zuwa ne bayan farmakin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankunan Bokkos da Barkin Ladi da Mangu na jihar yayin bikin kirsimeti.
Karanta wannan: Mutuwar Ghali Na’Abba ta firgita ni- Tanko Yakasai
Jirgin Shettima ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Yakubu Gowon da ke Heipang a Jos.
Ya jajanta wa wadanda suka rasa matsugunnan su, kuma suke killace a filin wasa na Bokkos.