Dattijon kasa, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana mutuwar tsohon kakakin majalisar wakilai ta 8, Ghali Umar Na’Abba a matsayin abin ban tsoro kuma mai firgitarwa.
Yakasai wanda ya zanta da manema labarai a Kano ya ce “Ghali da na ne, ya girma ya rike mukami, kuma kyawawan dabi’unsa sun sanya shi zama Kakakin Majalisa wanda ya mutu a lokacin da ake bukatar ayyukansa.”
Karanta wannan: Sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ta kasa a Gaza
Yakasai ya ci gaba da cewa Najeriya ta yi rashin wani jigo wanda ba za a gudunmawar da ya bawa dimokuradiyya ba.