Yanzu-yanzu: An rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo

The Acting Governor of Ondo State Lucky Aiyedatiwa is sworn in as governor on Wednesday December 27 2023
The Acting Governor of Ondo State Lucky Aiyedatiwa is sworn in as governor on Wednesday December 27 2023

Da yammacin Larabar nan ne aka rantsar da mukaddashin gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa, a mtsayin gwamnan jihar.

Bikin rantsuwar ya gudana ne a dakin taro na Cocoa dake ofishin gwamnan a Akure babban birnin jihar.

Babban mai shari’a Justice Olusegun Odusola shi ne ya saba masa layar rantsuwar da misalin karfe 5 da mintuna 18 na yamma.

Karanta wannan: Cikin hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya ziyarci Jihar Plateau

Daga cikin wadanda suka shaida rantsuwar akwai sauran alkalan jihar da manyan jami’an gwamnati da suka hadar da sakataren gwamnatin jihar.

Sauran su ne shugaban jam’iyyar APC na jihar da ‘yan majalisar dokokin jihar da sauran manyan mutane.

Rantsuwar ta sa ta biyo bayan mutuwar gwamna Oluwarotimi Akeredolu, da safiyar ranar Larabar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here