Kotu ta shigar da Gwarzo cikin karar da ake kalubalantar takararsa ta gwamnan Kano a NDC

Aminu Abdussalam Gwarzo 447x430

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta shigar da dan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin daya daga cikin wadanda ake kara a shari’ar da ke kalubalantar takararsa a zaben gwamna na shekarar 2027, tare da neman a cire sunansa daga jerin sunayen ’yan takarar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar.

Matakin ya biyo bayan zaman kotun, inda lauyan Gwarzo, Sagir Gezawa SAN, ya gabatar da bukatar neman kotun ta shigar da shi cikin wadanda ake kara a shari’ar.

Kotun ta amince da bukatar ne bayan masu shigar da karar sun janye takardar rantsuwar amsa bukatar da suka gabatar domin adawa da shigar da Gwarzo cikin shari’ar, lamarin da ya sa bukatar ta kasance ba tare da kalubale ba.

Bayan amincewa da bukatar, kotun ta umarci a gyara dukkan takardun shari’ar da aka riga aka gabatar domin su nuna cewa Gwarzo na daga cikin wadanda ake kara.

A yayin zaman kotun, lauyan jam’iyyar NDC, Dahiru Ibrahim, wadda ita ce ta biyu cikin wadanda ake kara, ya sanar da kotun cewa akwai wata bukata da suke son gabatarwa domin soke umarnin wucin gadi da ya hana INEC wallafa ko sauya sunayen dan takarar gwamna da jam’iyyar ta gabatar.

Sai dai kotun ta umurci cewa dole ne a fara gyara wannan bukata ta hanyar saka sunan Gwarzo a cikinta kafin ta saurare ƙarar.

An shigar da karar mai lamba FHC/KN/CS/440/2026 ne ta hannun wasu mambobin jam’iyyar NDC uku da suka hada da Garba Umar Isa, Yau Nasiru da Atiku Jamilu Abubakar, wadanda suka shigar da kara kan INEC da jam’iyyar.

Masu shigar da karar na kalubalantar fitar Gwarzo a matsayin dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar da kuma Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa, inda suke zargin an samu kura-kurai a tsarin tsayar da ’yan takarar.

Sun kuma zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, da yin tasiri wajen zaben ’yan takarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here