Kaduna: NDLEA ta gano wurin kera bindigu ba bisa ka’ida ba tare da kama mai ita

NDLEA NDLEA NEW

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun tarwatsa wata masana’antar kera bindigu ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Kaduna, inda suka kama mai ita tare da ƙwace bindigogin da aka ƙera a cikin gida da kayan aikin samar da makamai.

Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma na hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wani rahoton abubuwan da suka shafi miyagun ƙwayoyi da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.

An gudanar da samamen ne a yankin Sabon Garin Kangin da ke jihar, inda jami’an suka gano wata masana’anta da aka tanadar domin kera bindigu.

Babafemi ya ce samamen ya haifar da ƙwato bindigogin da aka riga aka ƙera da kuma wasu kayayyakin da aka tanada domin ƙera ƙarin makamai.

“A yayin wani samame da jami’an NDLEA suka gudanar a yankin Sabon Garin Kangin da ke Kaduna kwanakin baya, sun gano wata masana’antar kera bindigu, inda suka ƙwato bindigogin da aka riga aka ƙera da kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da ƙarin makamai, tare da kama mai masana’antar.”

Ya ce wannan samame ya ƙara tabbatar da alaƙar da ke tsakanin fataucin miyagun ƙwayoyi, shaye-shaye da sauran nau’o’in aikata laifuka.

“Wannan ya ƙara tabbatar da abin da aka riga aka sani, cewa akwai alaƙa tsakanin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, fataucinsu da sauran nau’o’in aikata laifuka.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here