Yanzu-Yanzu: ’Yan daba sun kai hari kan ayarin motocin Kwankwaso a Kano

Rabiu Kwankwaso

An samu arangama mai muni a karamar hukumar Bichi da ke Jihar Kano, bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo.

SolaceBase ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da tawagar ke gudanar da zagayen yaƙin neman zaɓe domin neman goyon bayan jama’a, bayan kammala ziyara a kananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai.

Da yake tabbatar da harin, mai magana da yawun dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Comrade Ibrahim Garba Shuaibu, ya ce sun samu bayanan sirri kafin su isa Bichi cewa wasu mutane sun tare hanya domin hana su gudanar da gangamin siyasa.

A cewarsa, bayan isarsu garin, sun fara lura da alamun jifan duwatsu, sannan jim kadan bayan sun wuce sakatariyar karamar hukumar, wasu gungun matasa dauke da makamai masu hadari suka fito suka farmaki ayarin motocinsu.

Shuaibu ya kara da cewa harin ya jikkata wasu daga cikin magoya bayansu tare da lalata motoci da dama.

Ya ce da kansa ya ga motoci kusan bakwai da aka farfasa gilasan madubin gabansu a wurin da lamarin ya faru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here