Gwamna Mohammed ya dakatar da Sarkin Lame tare da kafa kwamitin bincike

Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da Alhaji Aliyu Lame, Sarkin Lame da ke Karamar Hukumar Toro, bisa zargin aikata ba daidai ba.

Gwamnatin ta kuma amince da kafa kwamiti mai mutum 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamna Bala Mohammed shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Asabar a Bauchi.

A cewarsa, gwamnan ya amince da matakin ne bayan samun korafe-korafe a hukumance da kuma rahotannin bayanan sirri daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro.

Gidado ya ce zarge-zargen sun hada da tsoma baki ba bisa ka’ida ba a harkokin kula da filaye, karbar haraji ba tare da izini ba, tsoma baki a ayyukan kamfanonin hakar ma’adinai da wasu ayyukan da ake zargin sun saba wa ka’ida.

Ya kara da cewa ana zargin wadannan ayyuka sun haifar da zaman dar-dar a masarautar Lame tare da tayar da hankula kan zaman lafiya da tsaro.

Ya ce, “Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarauta ta taba bukatar Sarkin da ya yi bayani kan zarge-zargen, inda ya gabatar da amsoshinsa a rubuce.

“Amma gwamnatin ta yi la’akari da cewa bayanan da ya bayar ba su gamsar da ita ba, don haka ta ga ya dace a gudanar da bincike na musamman mai zaman kansa.”

Ya bayyana cewa kwamitin, wanda tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Sani Mohammed mai ritaya, zai jagoranta, ya kunshi wakilan hukumomin tsaro, ma’aikatun da abin ya shafa, Karamar Hukumar Toro da sauran hukumomin gwamnati.

A cewarsa, kwamitin yana da makonni uku domin gudanar da bincike kan zarge-zargen, nazarin takardun da suka shafi lamarin, gayyatar wadanda abin ya shafa da kuma mika rahotonsa tare da shawarwarinsa ga gwamnati.

Ya kuma ce dakatarwar mataki ne na gudanar da harkokin mulki na wucin gadi da aka dauka domin tabbatar da sahihancin binciken da kuma hana yiwuwar yin katsalandan ga shaidu da bayanan da ke hannun hukumomi.

Ya ce an umarci Sarkin da ya kasance a cikin Masarautar Lame, sai dai idan an ba shi izinin fita, tare da kaucewa tsoma baki a harkokin gudanarwa, na gargajiya da na hukuma na masarautar a tsawon lokacin dakatarwar.

Gidado ya kuma ce gwamnatin ta umarci Babban Jami’i a Masarautar, Alhaji Bala Gumau, da ya kula da harkokin gudanarwa na yau da kullum a masarautar na wucin gadi.

Ya ce gwamnatin ta bukaci mazauna Masarautar Lame da Karamar Hukumar Toro, shugabannin al’umma, masu rike da sarautun gargajiya da matasa da su kwantar da hankalinsu, su zauna lafiya, su kuma bi doka tare da ba hukumomin tsaro da kwamitin hadin kai.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here