Majalisar Kano ta ƙara wa’adin dakatarwa shugabannin ƙananan hukumomi 3 da watanni uku

Kano State House of Assembly 700x430

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙara wa’adin dakatarwar da aka yi wa shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Bagwai da Bebeji da ƙarin watanni uku.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labaran Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Litinin.

Shugabannin da aka dakatar sun haɗa da Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Alhassan Salisu na Bebeji da Abubakar Mustapha na Rogo.

Sani Shawai ya ce Majalisar ta kuma ƙara wa kwamitin wucin gadi da aka kafa domin binciken zarge-zargen da ake yi wa shugabannin watanni uku.

A cewarsa, tun da farko Shugaban Majalisar ya bai wa kwamitin watanni uku domin gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da rahotonsa ga Majalisar.

“Bayan cikar wa’adin farko, Majalisar ta ƙara wa’adin dakatarwar shugabannin ƙananan hukumomin da kuma wa’adin aikin kwamitin da wasu watanni ukun, domin bai wa kwamitin damar ƙara nazari kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar, kammala bincikensa da kuma miƙa rahotonsa ga Majalisar cikin watanni uku masu zuwa.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Majalisar ta dakatar da shugabannin ne a baya bayan zarge-zargen karya ƙa’idojin gudanar da harkokin mulki da ake yi musu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here