Gwamnatin tarayya ta fara shirin sayar da makarantun sakandare mallakin gwamnatin tarayya guda 110 da ake dasu a fadin kasar nan.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne kimanin shekaru ashirin bayan shirin da gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasango ta yi na sayar da makarantun na unity.
Kungiyoyin kwadago a karkashin kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ta Najeriya (ACSSN) wacce ta yi gargadin, a ranar Larabar da ta gabata ta shawarci duk masu sha’awar gudanar da makarantun sakandare da su gina nasu.
Sakatare Janar na ASCSN, Joshua Apebo, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ja hankali kan yunƙurin sayar da makarantun mallakin gwamnatin tarayya a duk faɗin ƙasar, yace masu san siya su gina nasu.