Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 na watan Disamba, da kuma 1 ga watan Janairun 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Kirsimeti, da rarraba kyautuka da kuma Sabuwar Shekara a faɗin ƙasar.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a Abuja.
Ministan ya taya mabiya addinin Kirista a Najeriya da ma sauran sassan duniya murnar bikin Kirsimeti, tare da taya dukkan ‘yan Najeriya barka da shigowar Sabuwar Shekara.
Ya bukaci Kiristoci da su yi tunani kan darussan ƙauna, zaman lafiya, tawali’u da sadaukarwa da aka nuna ta haihuwar Annabi Isa Almasihu, yana bayyana waɗannan dabi’u a matsayin ginshiƙai masu muhimmanci wajen haɗin kan ƙasa, juriya da zaman lafiya.
Ministan ya kuma ƙarfafa dukkan ‘yan ƙasa da su yi amfani da wannan lokacin bukukuwa wajen yin addu’a domin zaman lafiya, tsaro da ci gaban ƙasar, tare da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen bunƙasa ƙasa da ƙarfafa haɗin kai.
Ya kuma shawarci ‘yan ƙasa da su kasance masu bin doka, masu kula da tsaro, tare da yin bukukuwan cikin tsari da hankali, yana mai kira ga haɗin kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da hutun bukukuwa ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa ministan ya yi wa ‘yan Najeriya fatan murnar Kirsimeti da kuma Sabuwar Shekara mai albarka.













































