Gwamnan Jihar Ondo Aiyedatiwa ya kori Majalisar Zartaswa

Gwamnan, kori, majalisar,
Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartaswa ta jihar a ranar Laraba.Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Ebenezer Adeniyan...

Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartaswa ta jihar a ranar Laraba.

Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Ebenezer Adeniyan ne ya bayyana hakan, kazalika dukkan mambobin majalisar za su mika su ga manyan sakatarorin dindindin ko kuma babban jami’in gudanarwa a ma’aikatun su.

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga sun sake kai wani sabon hari Jihar Plateau

Ya kara da cewa sauran wadanda aka nada a siyasance kamar manyan mataimaka na musamman da masu taimakawa gwamna suma an sauke su daga nadin nasu.

“An umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu.

“Gwamnan ya godewa jami’an da abin ya shafa saboda aiyuka da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar Ondo,” in ji Adeniyan.

Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar Ondo a ranar 27 ga watan Disambar 2023 kamar yadda NAN, ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here