Tinubu ya gana da Blinken a ziyarar Afirka

Antony, tinubu, ziyara, gana
A ranar Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken wanda ke rangadin kasashen Afirka...

A ranar Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken wanda ke rangadin kasashen Afirka.

Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ne ya tarbi Blinken a bakin kofar fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayyar Abuja.

Blinken ya tattauna da tawagar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Tinubu.

Najeriya dai ita ce kasa ta 3 da ya kai ziyara a ziyarar da yake yi a nahiyar Afirka da nufin kulla kyakkyawar alaka da hadin gwiwa da nahiyar Afirka.

Karanta wannan: Gwamnan Jihar Ondo Aiyedatiwa ya kori Majalisar Zartaswa

Yayin da ya isa Abuja, ya samu tarba daga sakataren gwamnatin tarayya, Sen. George Akume da Tuggar.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya rawaito cewa Blinken ya fara ziyararsa ta 4 a Afirka a wannan makon, inda ya ziyarci Cabo Verde da Cote d’Ivoire da Najeriya da kuma Angola.

Muhimman abubuwan da suka sa a gaba a ziyarar dai sun hada da karfafa hadin gwiwar tsaro da inganta kiwon lafiya da kuma bunkasar tattalin arziki a yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here