Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta bankado wani shiri da jam’iyyar APC mai mulki ke yi na rage yawan mutanen da ke da katin zabe na dindindin a jihar ta hanyar saye tare da kwace su daga hannun wadanda suka mallakar na asali da nufin daluga hakkinsu na zabe .
Wannan dai nazuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta yi nuni da cewa a karon farko a tarihin mulki a jihar Kano, masu rike da madafun ikon Gwamnati ke mayar da al’amuran gwamnati tamkar na iyali musamman la’akari da nade-naden mukamai.
Sanarwar ta ce hakan na nuni da yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da babban nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa ta hanyar tada hankali, nuna son rai, da kuma wadatar da kai da yan uwa.
A cewar sanarwar hadin gwiwa da shugaban taron, Garba Diso da sakataren kungiyar Dokta Hamisu Sadi Ali suka sanyawa hannu a kokarin neman mafita cikin gaggawa kan barazanar da ake fuskanta, kwamitin ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta buga tare da liƙa sunayen duk masu katin zaben da ba a karba ba domin a wayar da kan masu haƙƙin mallakar su.
‘’Daga cikin sauran batutuwan da taron bitar ya fitar, ya yi nuni dacewa an samu rugujewar tsarin ilimi biyo bayan Rufe makarantun hadin kai da na kwana; rashin biyan kudin jarrabawar da gwamnatin jihar ta yi wa WAEC, NECO, da NBAIS; jinkiri da rashin biyan alawus na tallafin karatu ga daliban kasashen waje da na gida; da kuma samar da yanayi na rashin ilimi a cikin harabar makarantu ta hanyar gina shagunan kwana a makarantu kamar Jami’ar Arewa maso Yamma Kano,” in ji sanarwar.
‘’Saboda haka taron na nuna matukar damuwarsa kan ambaliyar ruwa da rugujewar gine-ginen da suka auku kwanan nan a kasuwannin Kantin Kwari da na Civic Centre wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi da sauransu.
“A karshe taron bitar ya bayyana goyon bayan jam’iyyar NNPP kacokan a jihar, inda ya jaddada cewa lallai zaben 2023 ya bambanta da wanda ya gabata, ya zama dole jam’iyyar ta yi duk abin da ya dace cikin tanadin doka don ganin zaben 2023 ya sami ‘yanci da adalci.”













































