Kotu ta yankewa Evans da abokan huldar sa zaman gidan yari  shekara 21

Evans in court 1
Evans in court 1

Babban Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun laifuka na musamman da ke zaman ta a Ikeja ayau Litinin ya yanke hukuncin daurin shekaru 21 a gidan dan-kande ga kasurgumin mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans da abokin sa Victor Aduba bisa samun su dumu dumu da laifin yin garkuwa da wani Sylvanus Hafia.

An zarge su da hada baki tare da yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar 23 ga watan Yuni 2014, akan titin Kara, Amuwo Odofin cikin Legas tareda bukatar basu $Milyan 2 amatsayin kudin fansa.

Rahotanni sun ce masu laifin sun ki amsa laifuka hudun da ake tuhumarsu da su dashi.

Alkalin kotun ya ce hukuncin zai zama izina ga sauran masu son aikata yin garkuwa da mutane sake-ba- kaidi.

Muna tafe karin bayani gaba kadan…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here