Majalisar dokokin jihar Imo ta tsige shugabanta, inda ta rantsar da sabon shugaba

Imo House of Assembly 750x430 1
Imo House of Assembly 750x430 1

Majalisar dokokin jihar Imo ta tsige shugabanta Kennedy Ibe, inda ta zabe Emeka Nduka a matsayin sabon shugaba.

Nduka shine dai shugaba na hudu a makalisar cikin shekara uku.

Mista Nduka shine mai wakiltar Ehime Mbano, wanda Chinelo Emeghara ya rantsar dashi a matsayin sabon shugaba.

Mataimakin shugaban majalisar, Amara Iwuanyanwu, da shugaban masu rinjaye Kanayo Onyemaechi  sun tayashi murnar samun kujerar.

An zabe tsohon shugaban majalisar ne a watan Nuwamba 2021, wanda shike wakiltar yakin Obowo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here