Majalisar dokokin Imo ta zabi sabon kakakin ta na hudu cikin shekaru hudu a ranar Litinin a Owerri.
Sabon kakakin Mista Emeka Nduka Na Wakiltar Ehime Mbano wanda ya maye gurbin Mista Kennedy Ibe Me Wakiltar mutanan Gundumar Obowo da ya yi murabus daga mukamin sa.
Rahotanni sun ce an tsige magabatan Ibe su biyu a shekarar 2020 da kuma 2021 akai akai.
An kuma antsar da Ibe Mai murabus a matsayin kakakin majalisar ne a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2021 biyo bayan tsige Mista Paul Emeziem bisa laifin aikata manyan laifuka.
Emeziem wanda ya karbi kujerar iko amatsayin kakakin Majalisa daga hannun Dr Collins Chiji a watan Nuwamba 2020 bayan da aka tsige shi saboda rashin da’a.
Sai dai Chiji ya roki majalisar da a cire shi daga cikin bayanan majalisar, a kuma rubuta shi a matsayin murabus inda nan take aka amince da bukatar.
An zabi shugaban majalisar na hudu, Nduka a ranar Litinin a wani zaman sirri wanda mataimakin kakakin majalisar, Mista Amarachi Iwuanyanwu ya jagoranta wanda ya bukaci a tantance kuma bayan ya karanta wasikar murabus din Ibe.
Shugaban masu rinjaye Mista Kanayo Onyemaechi me Wakiltar Imo ta yamma ya zabi Nduka wanda bukatar hakan ta samu goyon bayan Dr Uju Onwudiwe.
Saidai har izuwa lokacin hada wannan rahoto, Ibe bai bayar da dalilin murabus din sa ba.












































