Zargin ɓata suna: Dangote ya yi barazanar shigar da ƙarar wani ɗan kasuwa a Kaduna, tare da neman diyyar Naira Biliyan 100

Dangote Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bai wa wani ɗan kasuwa da ke jihar Kaduna, Injiniya Kailani Muhammad, wa’adin kwanaki bakwai da ya janye kalaman da ake zargin sun ɓata masa suna, ko kuma ya fuskanci ƙarar ɓatanci ta Naira biliyan 100 a gaban kotu.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 20 ga Disamba 2025, Dangote ya nemi a yi bayani a fili, a janye zarge-zargen, tare da bayar da cikakkiyar neman afuwa ga jama’a, bisa ikirarin da aka yi cewa ya shiga harkokin kasuwanci marasa tsafta a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers a shekarun 1980.

Wasiƙar, wadda lauyansa Dakta Ogwu James Onoja, Babban Lauyan Najeriya SAN na kamfanin lauyoyi na Onoja da ke Abuja, ya miƙa wa Kailani Muhammad, ta zarge shi da yin kalamai na ƙarya da suka cutar da mutunci da sahihancin Dangote, musamman game da tushen dukiyarsa a matsayinsa na mafi arziki a Afirka.

Bisa bayanin wasiƙar, kalaman da ake ƙorafi a kansu Injiniya Kailani Muhammad ne ya furta su a cikin wata hira da aka watsa a tashar Trust TV a ranar Laraba 17 ga Disamba 2025, a matsayin martani ga ƙorafin da Dangote ya kai ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa ICPC kan Injiniya Farouk Ahmed.

Wasiƙar, mai taken “Buƙatar bayani a fili, janyewa da neman afuwar jama’a kan wallafa kalaman ɓatanci da aka yi wa Alhaji Aliko Dangote GCON”, ta bayyana kalaman da aka watsa a talabijin a matsayin ƙarya, marasa hankali, masu tayar da hankali da kuma ɓatanci.

Lauyan Dangote ya jaddada cewa Dangote sanannen ɗan kasuwa ne a duniya wanda ya gina sunansa ta hanyar aiki tuƙuru, gaskiya, jajircewa da dagewa, yana mai cewa zarge-zargen sun yi mummunar illa ga matsayinsa a cikin al’ummar kasuwanci ta duniya.

Dangote ya musanta yin duk wata kasuwanci ko harkar sana’a a Port Harcourt a kowane lokaci, ciki har da shekarun 1980, yana bayyana ikirarin a matsayin ƙirƙirarru, marasa tushe da kuma masu nufin cutar da suna.

Wasiƙar ta yi gargaɗin cewa kalaman sun jefa Dangote cikin ƙiyayya, izgili da shakku a idon jama’a, tare da rage masa daraja a wurin abokan hulɗa, abokan kasuwanci da gwamnatocin ƙasashen da yake aiki.

Don haka ya buƙaci Kailani Muhammad ya yi bayani a fili a wannan dandali na Trust TV kan lokacin da kuma yadda Dangote ya shiga abin da ya kira ayyuka marasa tsafta a Port Harcourt, ya kuma janye kalaman gaba ɗaya tare da bayar da cikakkiyar neman afuwa ga jama’a da irin martabar da aka watsa hirar.

Haka kuma, Dangote ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 100 saboda lalata masa suna, tare da rubutaccen alƙawari daga Muhammad na gujewa sake yin duk wata magana ta ɓatanci a nan gaba.

Wasiƙar ta ƙara da cewa rashin bin wannan buƙata zai haifar da ɗaukar matakin shari’a nan take, ciki har da neman ƙarin diyyar azaba da kuma yiwuwar gurfanarwa ta ɓangaren laifin ɓatanci ta hannun hukumomin tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here