Jam’iyyar NDC za ta bayyana sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓenta na Ƙasa a ranar Litinin don tunkarar zaɓen 2027, za kuma ta gabatar da bayanin asusun kuɗaɗenta a taronta na uku na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa a Abuja.
Jam’iyyar ta ce za ta kuma miƙa takardun shaidar cin zaɓen fidda gwani ga ’yan takararta na shugaban ƙasa, Majalisar Tarayya, gwamnonin jihohi da kuma majalisun dokokin jihohi.
Read also: Sanata Shekarau ya karɓi katin zama ɗan Jam’iyar NNPP
An tsara gudanar da taron da ƙarfe 10 na safe a JD Event Centre, kan titin Kashim Ibrahim, daura da A-Class Park, Maitama Abuja.
Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyatr na Ƙasa, Osa Director, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
“Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da za a gudanar a taron shi ne fitarwa da kuma gabatar da bayanin asusun kuɗaɗen jam’iyyar ta hannun Ma’aji na Ƙasa. Wannan na nuna jajircewarmu wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
“A saboda haka, muna ƙalubalantar sauran jam’iyyun siyasa, musamman jam’iyyar APC mai mulki, da su yi koyi da wannan mataki na bayyana gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗensu. A wajen NDC, siyasa ba za ta ci gaba da tafiya irin yadda aka saba ba,” in ji shi.
Da yake bayani kan halin kuɗaɗen jam’iyyar, Director ya ce da kuɗaɗensu sun fi yawa idan ba don matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta ba, wanda ya ɗora alhakin faruwarsa kan gwamnatin APC.
Ya yi zargin cewa kusan kashi 80 cikin 100 na ’yan takarar jam’iyyar ba su da ikon biyan kuɗin fom ɗin nuna sha’awar tsayawa takara saboda talauci, yunwa da kuma matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
“Da a ce ba haka ba, da asusun kuɗaɗenmu ya fi ƙarfi. Sai dai, sabanin jita-jitar da ake yaɗawa a bainar jama’a, sakamakon tsananin talauci, yunwa da ƙangin rayuwa da manufofin tattalin arzikin gwamnatin APC marasa inganci suka haddasa, kusan kashi 80 cikin 100 na ’yan takararmu ba su iya biyan kuɗin fom ɗin nuna sha’awar tsayawa takara ba.
Read also: Murtala Garo ya taya Musulmi murnar Zagayowar Babbar Sallah
“Saboda haka, jam’iyyar ta bayar da fom ɗin kyauta ga irin waɗannan ’yan takara,” in ji shi.
A cewar sanarwar, Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen zai ƙunshi wakilai daga dukkan matakan zaɓe, ciki har da na shugaban ƙasa, Majalisar Tarayya, gwamnonin jihohi da majalisun dokokin jihohi.
Ta ƙara da cewa bayyana kwamitin zai ba jam’iyyar damar ƙara ƙarfafa tsarinta na yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
“NDC ta shirya tsaf kuma tana da ƙwarin gwiwar bai wa ’yan Najeriya shugabanci na gari da ƙasar ke buƙata. Sabuwar Najeriya mai yiwuwa ce. Za mu iya cimma hakan!”
Wannan shiri na bayyana Kwamitin na zuwa ne bayan da jam’iyyar ta ɗage bikin ƙaddamar da kwamitin, wanda tun farko aka tsara gudanarwa a ranar 20 ga Oktoba.
Jam’iyyar ta danganta ɗage taron da yawan ayyukan ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, da kuma wani muhimmin alƙawari da yake da shi a ƙasashen waje.
Daga bisani, an sanya ranar 26 ga Oktoba a matsayin sabuwar ranar gudanar da taron, tare da zaman Kwamitin Zartarwa na Ƙasa, inda ake sa ran jam’iyyar za ta yanke muhimman shawarwari kan shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027.
Read also: Ba zan kira ka da Kachalla ba saboda ka kira Tinubu da sunansa na farko – Shettima ga Atiku
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Moses Cleopas, ya taɓa yin watsi da zarge-zargen cewa NDC ba ta gudanar da ayyukanta ko kuma tana fama da rarrabuwar kawuna, inda ya jaddada cewa shugabancinta na nan daram wajen mara wa tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso baya.













































