Tawagar Gwamnatin Tarayya ta isa Saudiyya gabanin jana’izar Dantata

Aminu Dantata 750x430

Tawagar gwamnatin tarayya ta isa kasar Saudiyya domin karbar gawar marigayi hamshakin dan kasuwa kuma dattijon Najeriya Alhaji Aminu Dantata, gabanin binne shi a birnin Madinah mai alfarma.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Alhaji Dantata ya rasu ne a birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Asabar, yana da shekaru 94 a duniya.

Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Rabi’u Ibrahim ya fitar a ranar Litinin, ta ce tawagar da ta bar Najeriya da yammacin ranar Lahadi, ta isa Madina da sanyin safiyar Litinin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here