Taron Gangamin Kaduna: Su ne suka jawo yunwa — Tinubu ya caccaki abokan hamayya

President Bola Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗora alhakin yunwa da talauci a Najeriya kan abokan hamayyarsa na siyasa, yana mai cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin magance waɗannan matsaloli.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees, wanda aka fi sani da Kaduna Township Stadium, da ke Jihar Kaduna, gabanin babban zaɓen 2027.

“Ina da hujja. Ina jin abokan hamayyata suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya jawo su? Su ne suka jawo! Su ne suka jawo yunwa, su ne suka jawo talauci. Mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su,” in ji shugaban ƙasar.

Ya kuma kare tarihin ayyukan gwamnatinsa dangane da biyan albashi, tare da yabawa gwamnonin jihohi bisa ayyukan da suke gudanarwa, yana mai cewa suna samun ci gaba a jihohinsu.

“Muna biyan albashi a kan lokaci. Gwamnoninmu suna aiki. Ina alfahari da su. Suna kawo ci gaba,” in ji Tinubu.

Shugaban ƙasar ya gode wa al’ummar Jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, yana mai cewa ƙuri’un da suka ba shi sun taimaka wajen zama shugaban ƙasa.

“Kun ba ni farin cikin tunawa da nasarar da kuka ba ni ta zama shugaban ƙasa. Na sake dawowa ne domin in gode muku,” in ji shi.

Tinubu ya kuma roƙi ’yan Najeriya su sake ba shi damar yin wa’adi na biyu, yana mai cewa yana son ci gaba da tabbatar da alƙawuran da ya ɗauka na wadata, dorewar manufofi, ci gaba da bunƙasa ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here