APC ta fitar da jerin Jihohi 12 da Tinubu zai halacci gangamin ta

Tinubu Tinubu Tinubu 678x430

Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 a faɗin ƙasar nan, wanda ya ƙunshi jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

A ranar Laraba ne Shugaba Bola Tinubu, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC (PCC) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa ba zai samu damar halartar dukkan tarukan gangamin ba, domin ba ya son barin ayyukan gwamnati a gefe.

An tsara gudanar da gangamin ne daga watan Oktoba na shekarar 2026 zuwa farkon watan Janairun 2027, inda jihar Legas za ta karɓi babban taron rufe gangamin a ranar 9 ga Janairu, 2027.

Sai dai, bisa ga jadawalin da jam’iyyar ta fitar a ranar Alhamis, ana sa ran Shugaba Tinubu zai jagoranci gangamin neman sake zaɓensa a jihohi 12, ciki har da Kaduna, inda jam’iyyar mai mulki za ta ƙaddamar da gangamin a hukumance a ranar 24 ga Oktoban 2026.

Jadawalin ya nuna cewa Shugaba Tinubu zai kuma jagoranci gangamin APC a Fatakwal, jihar Rivers, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 7 ga Nuwamba.

Haka kuma, zai halarci gangamin a jihar Filato a ranar 14 ga Nuwamba, sannan ya je Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar 21 ga Nuwamba.

Haka zalika, ana sa ran shugaban ƙasar zai jagoranci gangamin a jihar Borno a ranar 25 ga Nuwamba, da kuma jihar Enugu a ranar 28 ga Nuwamba.

Ana kuma sa ran Tinubu zai jagoranci gangamin a Sakkwato a ranar 5 ga Disamba, kafin daga bisani ya jagoranta a Asaba a babban birnin jihar Delta, a ranar 12 ga Disamba.

Tinubu zai jagoranci gangamin APC a Kano, wadda take cikin jihohin da ke da yawan masu zaɓe a Arewa, a ranar 17 ga Disamba.

A ranar 29 ga Nuwamba ne kuma jihar Bauchi za ta karɓi tawagar gangamin APC, inda ake sa ran shugaban ƙasar zai jagoranta.

Haka kuma, shugaban ƙasar zai jagoranci gangamin a Yola, babban birnin jihar Adamawa, wadda ita ce jihar da babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, ya fito, a ranar Litinin 4 ga Janairun 2027.

Za a gudanar da babban taron rufe gangamin a jihar Legas a ranar Asabar, 9 ga Janairun 2027.

Sauran jadawalin gangamin APC

Sauran jihohin da za su karɓi gangamin da ranakun gudanar da shi sun haɗa da:

Jihar Imo (Owerri) 30 ga Disamba, Jihar Ondo (Akure) 11 ga Nuwamba, Jihar Katsina 2 ga Disamba, Jihar Akwa Ibom (Uyo) 18 ga Nuwamba, Jihar Benue (Makurdi) 30 ga Nuwamba, Jihar Ogun (Abeokuta) 3 ga Disamba, Jihar Anambra (Awka) 19 ga Nuwamba, Jihar Gombe 3 ga Nuwamba, Jihar Kebbi 17 ga Nuwamba sai Jihar Edo 12 ga Nuwamba da Jihar Kwara 10 ga Disamba.

Sauran sune Jihar Osun 9 ga Disamba, Jihar Abia: 7 ga Disamba, Jihar Yobe 16 ga Nuwamba, Jihar Zamfara 14 ga Disamba, Jihar Bayelsa 15 ga Disamba, Jihar Neja 16 ga Disamba, Jihar Ekiti 5 ga Nuwamba, Jihar Ebonyi 9 ga Nuwamba, Jihar Taraba 19 ga Disamba, Jihar Jigawa 10 ga Nuwamba, Jihar Cross River 2 ga Nuwamba, Jihar Kogi 8 ga Disamba, Jihar Nasarawa 4 ga Nuwamba da kuma Jihar Adamawa 4 ga Janairu, 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here