’Yan Bindiga sun kashe Jami’in Shige da Fice, tare da jikkata wani a Neja

Nigeria Immigration scaled

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani jami’in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) yayin da yake gudanar da sintirin sa ido a yankin Tunga Taya–Woro da ke Jihar Neja, sun kuma jikkata abokin aikinsa sosai.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mataimakin Kwanturola, DCI Akinsola Akinlabi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewarsa, hukumar ta ce, “Muna baƙin cikin sanar da wani mummunan hari da aka kai wa jami’anmu biyu na ofishin kula da shige da fice na Wawa, a yankin Tunga Taya–Woro da ke Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’i guda tare da jikkata wani sosai.”

Akinlabi ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, 6 ga Oktoban 2026, da misalin ƙarfe 11:30 na safe, lokacin da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa jami’an biyu hari yayin da suke gudanar da sintirin sa ido.

Jami’in da ya rasa ransa mai suna ASI I, I.U. Babangida.

Ɗayan jami’in kuma, mai suna Sufeto A.K. Musa, ya samu munanan raunuka, amma ya yi nasarar tserewa daga wurin harin, kuma a halin yanzu yana karɓar magani.

Sanarwar ta ce an riga an yi jana’izar marigayin bisa tsarin addinin Musulunci.

“Hukumar ta girmama sadaukarwar jami’in da jajircewarsa wajen gudanar da aikinsa.”

Haka kuma, hukumar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamacin da abokan aikinsa.

Ta ce tana jajantawa iyalan mamacin, abokan aikinsa da sauran waɗanda rasuwarsa ta shafa, tare da yi wa jami’in da ya jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Hukumar ta kuma tabbatar wa iyalan jami’an biyu cewa za ta ci gaba da ba su tallafi da taimako a wannan lokaci mai wuya.

Dangane da ƙoƙarin kamo waɗanda suka kai harin, hukumar ta ce tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Neja da sauran hukumomin tsaro domin gano waɗanda suka aikata laifin tare da kama su domin su fuskanci hukunci.

“Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ba za ta bari wannan mummunan lamari ya karya mata gwiwa ba, kuma tana sake jaddada ƙudurinta na kare iyakokin ƙasar nan.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here