Shige da Fice: Burtaniya Za Ta Hana Daliban Najeriya, Da Sauransu Shiga Da Iyalan Su Kasar.

Kasar Burtaniya ta shirya tsaf domin fidda sanarwar wasu sabbin takunkumai da za su iya hana daliban Najeriya da sauran ‘yan kasar da ke karatu a Burtaniya kai iyalansu.

A cewar wani rahoto na musamman da jaridar The Sun UK ta fitar, a wannan makon, tace za a sanar da wannan umarni nan bada jimawa ba.

Rahotanni sun ce wannan haramcin ba zai shafi ɗaliban PHD ba, waɗanda kwasa-kwasansu yawanci suna ɗaukar shekaru 3 zuwa 5, in ji Gidan watsa labarai na Burtaniya.

Wannan ya biyo bayan rahotannin da ke cewa tururuwar yin hijira zuwa Burtaniya ta karu zuwa miliyan 1, inda ‘yan majalisar Tory suka nemi Firayim Minista, Rishi Sunak, “ya amsa rokon su.”

Gidan jaridar ya ba da rahoton cewa “Ana sa ran Rishi Sunak zai fito na fito da bakin haure – yana mai nuni da cewa alkalumman da ya gada ne tun daga shekarar da ta kare a Disamba 2022 – watanni biyu bayan ya zama Firaminista.

“Dalibai sun kawo ‘yan uwan su 135,788 zuwa Burtaniya a bara – sau tara fiye da na 2019.

“A bara, daliban Najeriya 59,053 sun kawo ‘yan uwa sama da 60,923.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here