Tsohon Manajan Daraktan NPA, Aminu Dabo ya fice daga APC

Aminu Dabo 387x430

Wani jigo a jam’iyyar APC, kuma shugaban kwamitin wakilan jam’iyyar a ƙaramar hukumar Dambatta ta Jihar Kano, Arc. Aminu Dabo, ya fice daga jam’iyyar mai mulki nan take.

A cikin wata wasiƙar barin da ya rubuta ranar 7 ga Oktoban 2026, kuma ya sanya wa hannu da kansa, wadda ya aikewa shugaban APC na mazabar Dambatta Gabas, Aminu Dabo ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan yin la’akari da wasu dalilai na ƙashin kansa da kuma tsare-tsarensa na gaba.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Abdullahi Othman, ya fitar ranar Laraba, ya kuma aikewa SolaceBase, an tabbatar da cewa tsohon Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Aminu Dabo, ya miƙa takardar barin nasa a hukumance, inda ya janye kasancewarsa cikakken ɗan jam’iyyar.

Sanarwar ta ce tuni ya miƙa wasiƙar ga jami’an jam’iyyar da abin ya shafa a garin Dambatta domin ɗaukar matakin da ya dace.

“Ina ci gaba da godiya bisa kyakkyawar alaƙar da na more, tare da jin daɗin ƙwarewar da na samu a lokacin da nake yi wa jam’iyyar hidima.”

Arc. Aminu Dabo ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar bisa damar da suka ba shi da kuma amincewar da suka nuna masa wajen bayar da gudummawa ga ci gaba da bunƙasar jam’iyyar a lokacin da yake cikinta.

“Ina matuƙar godiya bisa goyon baya da damar da na samu daga shugabannin jam’iyyar,” in ji shi a ƙarshen wasiƙar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here