Tinubu ya ba da uzuri kan yawon kamfen na APC, “ba zan bi ku ko’ina ba”

Asiwaju Bola Tinubu 560x430

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shaida wa mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC cewa kada su yi tsammanin zai riƙa raka su zuwa dukkan wuraren da za su gudanar da gangami gabanin babban zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa dole ne ya mayar da hankali kan gudanar da mulki da kuma nauyin tattalin arzikin ƙasar dake kansa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC a Abuja, inda ya buƙaci mambobin kwamitin su isar da saƙon jam’iyyar ga ’yan Najeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi, yayin da shi kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati.

Shugaban ƙasar ya ce ya amince da damuwar cewa buƙatun yaƙin neman zaɓe bai kamata su ɗauke hankalinsa daga gudanar da mulkin ƙasar ba, yana mai cewa Najeriya na buƙatar kulawarsa a halin yanzu.

“Kun gargaɗe ni da kada in bari wahalhalun yaƙin neman zaɓe su ɗauke hankalina daga gudanar da mulki, na ji wannan gargaɗi. Na amince gaba ɗaya da matsayar da kuka ɗauka. A yanzu Najeriya na buƙatar kulawa sosai,” in ji Tinubu.

Ya buƙaci mambobin kwamitin da su yafe masa rashin raka su zuwa dukkan wuraren kamfen, yana mai cewa gwamnatinsa na da kuɗaɗen da za ta biya da kuma wajibai na kuɗi da take da su a ƙasashen duniya.

“Don haka, za ku yafe min rashin zuwa ko’ina tare da ku, muna da kuɗaɗen da za mu biya. Masu binmu bashi na Amurka ba za su jira ba,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya kuma ce gwamnati na buƙatar jawo hankalin masu zuba jari waɗanda za su yi dogon zangon zuba jari a Najeriya tare da bayar da gudummawa ga kyakkyawar makomar ’ya’yan ƙasar.

“Muna son waɗannan masu zuba jari su zo, su zauna a nan na dogon lokaci, su zuba jari domin makomar ’ya’yanmu,” in ji shi.

Sai dai shugaban ƙasar ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa zai ci gaba da samun lokaci don tattaunawa da su kai tsaye, duk da cewa kwamitin yaƙin neman zai jagoranci gangamin neman goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar.

“Duk da haka, zan ci gaba da samun lokaci don yin magana kai tsaye da ’yan Najeriya, yayin da ku za ku jagoranci gangamin a jihohi da ƙananan hukumomi,” in ji shi.

Tinubu ya bayyana ƙaddamar da kwamitin a matsayin wani abu da ya wuce harkar yaƙin neman zaɓe kawai, yana mai cewa hakan na nuna sabunta alƙawarin da suka ɗauka ga ’yan Najeriya da kuma nauyin da ke kan jam’iyyar mai mulki.

“Ba wai kawai mun taru ne domin ƙaddamar da kwamiti ba. Mun taru ne domin sabunta wata yarjejeniya. Yarjejeniya da al’ummar Najeriya da kuma babban nauyin tarihi da suka ɗora mana a matsayin jam’iyyar da ke mulkin Najeriya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ana sa ran kwamitin zai isar da hangen nesa, nasarorin da gwamnati ta samu da kuma shirye-shiryenta ga masu zaɓe a faɗin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here