Dakatar da ni da aka yi raina umarnin kotu ne, ina nan daram a jam’iyyar NNPP – Rurum

Kabir Alhassan Rurum

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure a majalisar wakilai Kabiru Alhassan Rurum, ya yi watsi da matakin dakatar da shi da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen jihar Kano ta yi.

Rurum ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a Kano ranar Litinin cewa dakatarwar da aka yi masa ba ta da tushe balle makama kuma a raina kotu ne, yana mai cewa zai ci gaba da zama dan jam’iyyar.

Rurum ya ce shi da sauran abokan aikin sa da ake zargin an dakatar da su daga wani bangare ne na NNPP.

Ci gaban karatu: Rikicin siyasa: Wani tsagi na NNPP ya ki amincewa da dakatar da ‘yan majalisar tarayya hudu a Kano

Ya zargi shugabannin jam’iyyar NNPP na Kano da yin watsi da hukunce-hukuncen shari’a, inda ya bayyana cewa su ba halastattun shugabannin jam’iyyar ba ne.

Rurum ya bayar da misali da hukuncin da kotu ta yanke wanda ya yi watsi da ikirarin nasu ya kuma tabbatar da cewa sun kai shi wata babbar kotun Abia, inda ya kara da cewa har yanzu kotun ba ta yanke hukunci kan lamarin ba.

Kano: NNPP ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya 4 bisa zargin yi mata zagon ƙasa

Ya yi zargin cewa an gayyaci shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugabanta na kasa, Rabi’u Kwankwaso, zuwa wurin Sanata Kawu Sumaila daya daga cikin ‘yan majalisar da abin ya shafa, daurin auren ‘ya’yansa amma suka zabi ba za su halarta ba.

Rurum ya yi watsi da dakatarwar da cewa ba shi da ma’ana, ya kuma jaddada cewa dakatarwar ta shafi bangaren da suka fitar ne kawai, domin bangaren sa ba shi da alaka da su.

Wannan rikici ya kara fito da tabarbarewar da ke tsakanin jam’iyyar NNPP ƙarara, inda ake ci gaba shari’a da kuma takun sakar siyasa da ke kara fadada rarrabuwar kawuna tsakanin bangarorin biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), reshen jihar Kano, ta sanar da dakatar da mambobinta hudu daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar nan bisa wasu zarge-zarge na yiwa jam’iyyar zagon ƙasa.

Shugaban jam’iyyar na jiha Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya sanar da dakatarwar da yake zantawa da manema labarai, tare da bayyana sunan Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Rogo da Kabiru Alhassan Rurum a matsayin wadanda aka dakatar.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here