Rikicin siyasa: Wani tsagi na NNPP ya ki amincewa da dakatar da ‘yan majalisar tarayya hudu a Kano

L R Kawu Sumaila Sani Rogo Ali Madakin Gini and Alhassan Rurum 750x430

Shugabancin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a karkashin Sanata Mas’ud El Jibril Doguwa, ya musanta rahoton dakatar da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar nan guda hudu, tare da jaddada cewa matakin bai dace ba.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa a ranar Litinin ne wani bangare na jam’iyyar da Hashimu Dungurawa ke jagoranta ya sanar da dakatar da Sanata Kawu Sumaila daga (Kano ta Kudu), da kuma ‘yan majalisar wakilai Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar Rano da Kibiya, sai Ali Madakin Gini mai wakiltar karamar hukumar Dala, da Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar karamar hukumar Rogo da Karaye, bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon ƙasa.

Sai dai a wani martani da suka mayar, bangaren Doguwa ya yi watsi da batun dakatarwar da aka yi, inda suka bayyana cewa Dungurawa ba shi da hurumin daukar wannan mataki.

“Jam’iyyar ba ta dakatar da kowa ba. Hashimu Dungurawa yayi kuskure. Idan har za a dauki irin wannan hukunci, to ni ne zan yi hakan.”

Labari mai alaƙa: Kano: NNPP ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya 4 bisa zargin yi mata zagon ƙasa

Da yake ba da misali da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, Doguwa ya jaddada cewa ‘yan majalisar da abin ya shafa ‘yan kwamitin zartarwa ne (NEC), kuma babu wani ɓangare da ya ke da hurumin dakatar da su.

“Ina so mutane su gane cewa Kwankwasiyya kungiya ce ba jam’iyyar siyasa ba, kuma tuni ‘yan majalisar suka bar Kwankwasiyya. Duk da haka, sun ci gaba da zama mambobin NNPP.

Ya kuma kara tabbatar da cewa, a bangaren NNPP, an kori shugaban Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf shi ma yake matsayin dakatacce.

Sanata Mas’ud El Jibril Doguwa ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu domin suna kokarin hada kan jam’iyyar da kuma daidaita.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here