Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Sulaiman daga kan kujerar sa.
Kotun mai alakalai uku a zamanta na ranar Juma’a ta kuma bada umarnin da’a sake zabe a mazabar Bauchi ta tsakiya inda dan majalisar ke wakilta.
Tace za’a sake zaben ne a rumfunan zabe guda goma dake mazabar Dan-majalisar.
A Zaben dai da aka gudanar na ranar 18 ga watan maris, Sulaiman wanda shi ne dan-takarar Jam’iyyar PDP ya yi nasara da kuri’u dubu 18 da 866, yayin da Khalid Abdulmalik Ningi, na jam’iyyar APC ya zama na biyu da kuri’u dubu 15 da 65.
Tun da farko dai Abdulmalik, ya nufi kotun sauraron kararrakin zabe, inda yake kalubalantar nasarar Abubakae Sulaiman din sai dai kotun ta yi watsi da korafin na sa, sai dai bayan hukuncin kotun farkon ne kuma sai ya daukaka kara.
Kazalika Abubakar Sulaiman, tab akin mai Magana da yawun sa Abdul Burra, ya bayyana hukuncin da cewa ba sabon abu bane a siyasa.
Ko da yake yace hukuncin bai musu dadi ba, amma dai duk da haka yana kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalin su wannan ba wani abu bane.












































