Mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin mota a jihar Kwara 

Accident road
Accident road

Mutane 8 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a Oke-Onigbin kan babbar hanyar Omu-Aran zuwa Ilorin a karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara ranar Juma’a.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar Kwara, Stephen Dawulung, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kakakinta, Busari Basambo ya fitar ranar Asabar a Ilorin, ya ce hatsarin ya faru ne cikin dare.

Dawulung ya ce an ajiye wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti domin kula da lafiyarsu.

Ya kara da cewa hatsarin na da nasaba da wuce gona da iri wajen tuki.

Ya shawarci masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiye da daddare da wuce gona da iri sannan kuma su tabbatar sun huta na tsawon mintuna 30 bayan kowane awa hudu na tukin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here