Yan Bindiga Sun Sace Sama Da Mutane 100 Saboda Rashin Biyan Harajin Naira Miliyan 50 A Zamfara

bandits
bandits

‘Yan ta’adda sun sace sama da mutane 100 mazauna garin Mutunji da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, a arewa maso yammacin Najeriya.

An tattaro cewa ’yan bindiga sun kai harin ne a daren Juma’a bayan sallar isha’i.

Mazauna yankin sun shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa ‘yan bindigar sun kasance masu biyayya ga Damina, dan ta’addan da ke yankin. Sun ce ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura inda suka kewaye mutanen kauyen kafin su kai su daji.

An gano cewa an sace su ne saboda rashin biyan harajin Naira miliyan 50 da mutanen kauyen ke bawa Damina a matsayin haraji.

Babu wata sanarwa daga jami’an tsaro game da harin da aka kai a daren Juma’a a garin Mutunzi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here