Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mista Femi Gbajabiamila ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an fara shirin bada lamuni ga dalibai a watan Janairun 2024 domin baiwa daliban Najeriya damar samun kudaden da zasu taimaka musu wajan samun ilimi.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne a Legas ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da wata lacca mai taken “Karfafa Matasan Nijeriya gwaiwa Kan Tattalin Arziki ” taron taro karo na 35.