Ku Dakatar da Bawa Jihohin Najeriya 36 Bashi – SERAP Ta Shawarci Bankin Duniya

world bank 1
world bank 1

Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arziki SERAP ta yi kira ga bankin duniya da ya dakatar da bayar da lamuni ga jihohi 36 na Najeriya bisa zargin karkatar da kudaden ta hanyar da bai dace ba.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Nuwamba, 2023, kungiyar ta bukaci shugaban bankin, Ajay Banga, da ya gaggauta gudanar da bincike kan yadda gwamnonin jihohin kasar nan 36 suka kashe kudaden lamuni da sauran ababen more rayuwa da kuma dakatar da duk wani lamuni da za’a kara basu.

Mataimakin darakta SERAP Kolawole Oluwadare ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa bankin Duniya da abokan huldarsa ba za su iya ci gaba da bayar da tallafi da sauran kudade ga wadannan jihohin da ake samun sahihan zarge-zargen almundahana ko karkatar da kudaden  ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here