Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahamad Tinubu ya gana da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yana daya daga cikin wadan da suka fafata da Tinubu a zaben shuganan kasa da aka kammala a watan Fabarairun shekarar 2023.
Kwankwaso wanda yai takarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, ya ci jihar Kano ne kadai, inda ya kayar da jam’iyya mai mulki APC.
Majiyar mu ta bayyana mana cewa sun shafe awanni suna ganawa da junansu a ranar Litinin a paris babban birnin kasar Farance.
“Zababben shugaban kasar da kwankwaso sun shafe sa’a 4 suna ganawa a pari a ranar Litinin. An fara ganawar da misalin karfe 12: 30 har zuwa 4:45. Ganawar ta su ta sami halartar shugaban majalisar wakilan Najeriya, Inda Abdulmumin Jibrin ya raka kwankwaso.” Inji majiyar mu.
“Sen Oluremi Tinubu itama ta samu damar ganawa da matar kwankwaso hajiya salamatu, inda suka tau-tau na a kan tsohowar rayuwar su su ta baya tun lokacin da mazajan suna majalisa a shekarar 1992, dakuma sauran hirar raki da suka shafi cigaban Najeriya, da kuma kokarin mijinta na gayyatar kwankwaso cikin gwamnatin sa, inda kuma kwankwason ya amsa gayyatar.
Mujiyr ta mu ta kara da cewa Tinubu na kokarin sasanta gwamna Ganduje da kwamskwaso.













































