2023: TNM, kungiyar siyasa karkashin jagorancin Kwankwaso, zasu marawa jam’iyyar NNPP baya

E6C45429 8EB0 474E 8A4A 71707267FAFE
E6C45429 8EB0 474E 8A4A 71707267FAFE

Kungiyar siyasa ta TNM karkashin jagorancin Sen. Rabi’u Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ta dauki jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), a matsayin jam’iyyar siyasa da zasu marawa baya domin cimma burinsu na samun madafun iko a zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban kwamitocin riko na jam’iyyar na kasa, AVM John Ifeimeje mai ritaya, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da shugabannin kungiyar Protem suka gudanar a ranar Litinin a Abuja.

TNM, wanda aka kaddamar a ranar 22 ga watan Fabrairu, wata kungiya ce ta ‘yan Najeriya masu nuna damuwa da kishin kasa daga dukkan jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja wadanda suka damu da halin da al’ummar kasar ke ciki kuma suka amince su hada kai don cin zabe a 2023.

Ifeimeje ya ce, a bisa manufofin kungiyar TNM, kungiyar ta kudiri aniyar hada kai, tare da daukar jam’iyyar NNPP domin ci gaba da fafutukar ceto kasar nan daga zargin tafka magudi, rashin iya aiki da rashin hukunta su, rashin tsaro da rashawa da talauci da dai sauransu.

Ifeimeje ya ce tuni aka kammala hadewar bangarorin biyu na masu kishin kasa a Najeriya.

A cewar Ifeimeje, kwamitin riko na kasa ya kunshi Dokta Boniface Aniebonam a matsayin shugaban kwamitin amintattu (BOT), Ifeimeje a matsayin shugaban hadakar, Sanata Suleiman Hunkuyi a matsayin mataimakin shugaba.

Sauran a cewarsa, sun hada da Oladipo Olayoku a matsayin sakataren kasa, Dr Ajuji Ahmed a matsayin mataimakin sakataren kasa, Maj. Agbo, sakataren yada labarai na kasa, Farfesa Rufa’I Alkali, sakataren tsare-tsare na kasa, Farfesa Bem Angwe, mai baiwa kasa shawara kan harkokin shari’a.

Haka kuma a cikin jam’iyyar akwai Cif Abba, Sakatariyar harkokin kudi ta kasa, Mrs Elizabeth Aliu, mai binciken kudi na kasa, Hajiya Maryam Yasin, shugabar mata ta kasa, Mohammed Dansada, shugaban matasa na kasa, da Ann Obute, sakatariyar jin dadin kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here