Mista Abdulkadir Ahmad, Babban Darakta mai kula da iskar gas da wutar lantarki na Kamfanin Man Fetur na Najeriya, ya bayyana cewa, Aikin bututun iskar gas daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKKP), ya kai kashi 73.3 bisa 100 na kammala aikin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa aikin na AKKP ya ya samu amincewar gwamnatin tarayya da nufin jigilar iskar gas daga Ajaokuta da ke jihar Kogi zuwa Kano a jihar Kano ta wasu jihohi da birane.
Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Kaduna lokacin da yake jawabi a matsayin babban bako mai jawabi a wajen taron jin ra’ayin jama’a tare da karrama Mista Suleiman Umaru, Sarkin Lere a Jihar Kaduna, wanda kungiyar injiniyoyo ta Najeriya (NSCHE) ta shirya.
Ahmad, wanda ya samu wakilcin Mista Emmanuel Ibookwuwe, Janar Manaja na Kamfanin Gas na Najeriya, ya yi magana a kan maudu’in Tsare-tsaren samar da Gas a jihohin Arewa da ma Najeriya gaba daya.”
Har ila yau, Mista Idris Bugaje, babban sakataren hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) wanda shi ne shugaban taron, ya bayyana aikin AKKP a matsayin wani muhimmin aiki, inda ya kara da cewa bayan kammala aikin zai magance matsalar rashin isasshiyar wutar lantarki.
Tun da farko a jawabin maraba, Mista Saidu Mohammed, shugaban NSCHE na kasa, ya bayyana cewa, duk da cewa an fuskanci kalubale a bangaren iskar gas da sauran bangaren suka dogara da shi, yana da kwarin gwiwar cewa za a samu sakamakon da ake bukata.
Mohammed ya taya wadanda suka shirya taron murna, sannan ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu daga abubuwan da aka gabatar a wajen taron.













































