Cikin Hotuna: Dubban mabiya Darikar Qadiriyya sun hallara a Kano domin bikin Waliyyai karo na 75

WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.25 750x430

Dubban mabiya darikar Qadiriyya sun taru a Kano a ranar Asabar domin gudanar da bikin Waliyyai karo na 75.

Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara, jagoran darikar Qadiriyya a nahiyar Afrika, ne ya jagoranci taron wanda ya samu halartar mabiya daga sassa daban-daban na Najeriya da ma ƙasashen waje.

Solacebase ta rawaito cewa, ana shirya wannan biki a kowace shekara ta hannun Darul Qadiriyya da ke hedikwatar darikar a Najeriya domin tunawa da ranar haihuwar Sheikh Abdulqadir Al-Jilani, wanda ya kafa wannan darika.

Dubban mabiya Ɗariƙar sun yin jerin gwanon a titunan Kano, inda mabiya daga masallatai da makarantu daban-daban suka fito da launuka iri-iri, suna nuna haɗin kai, imani da ƙauna ga Allah.

A wani ɓangare na bikin, Sheikh Qaribullahi Kabara ya ziyarci wasu wurare a Kano ciki har da filin Waliyyai, makabartar mahaifinsa, inda ya tsaya a wurare daban-daban domin yin addu’o’i na musamman ga al’umma kafin ya dawo Darul Qadiriyya.

Bikin ya gudana cikin yanayi na shauƙi, inda aka rufe shi da rera wakokin addini na yabon Allah, lamarin da ya ƙara sanya gagarumar sha’awa da zurfin ma’ana a wannan al’ada ta shekara shekara.

WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.22 768x576 WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.24 768x432 WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.28 768x576 WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.27 768x576 WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.25 750x430 WhatsApp Image 2025 10 04 at 11.23.31 768x576

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here