Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin tsohon gwamnan babban nakin Kasa CBN

Emefiele, EFCC, hukuma, bankado, zargi
Hukumar EFCC ta sake bunciko shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele da aka dakatar bisa tuhumar sa da zamba a wata babbar kotu da ke Abuja...

Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele, kan kudi naira miliyan 300 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

Mai shari’a Hamza Mu’azu ne ya bayar da belin, tare da sharadin karbe takardun tafiyar tsohon gwamnan babban bankin.

Godwin Emefeile wanda bai halarci zaman kotun da aka yi na bayar da belin nasa ba, an sanya masa sharadin sai ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, da suke da takardun mallakar gida ko filaye a unguwar Maitama da ke Abuja.

Cikin sharudan kotun da ta gindaya na ba da belin ta ce sai Emefeile ya bayar da takardun tafiye-tafiyensa ga magatakardan kotun, sannan duk zirga-zirgar da zai yi ba zai fita daga kwaryar birnin Abuja ba.

Har yanzu dai yana tsare a gidan yarin Kuje da ke Abuja, zuwa lokacin da zai cika sharudan da aka zayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here