An wayi gari cikin yanayi na ce ce ku ce da tafka muhawara dangane da wani kwafin takaradar shari’ar da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna cewa kotun ɗaukaka ƙara ta bai wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf nasara a shari’ar da APC ke kalaubantarsa.
Tun bayan fitar kwafin takaradar shari’ar wadda ake cewa kotun daukaka kara ce ta fitar kan hukuncin da ta yi kan zaɓen gwamnan, ake ta samun mabambanta ra’ayoyi musamman tsakanin bangarori biyun da ke cikin shari’ar.
A ranar Juma’a ne kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta kori karar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar gabanta, yana kalubanlantar hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Kotun kararrakin zaben ta ce Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, ba Abba Kabir Yusuf na NNPP ba.
Sai dai gwamna Abba Kabir da jam’iyyarsa ta NNPP sun garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
A zaman yanke hukuncin da kotun ta yi ranar Juma’ar da ta gabata dukkan alkalan kaotun uku sun ce Nasiru Yusuf Gawana an APC ne ya lashe zaɓen, kasancewar Abba Kabir Yusuf ya yi takarar gwamnan ne ba tare da kasancewa karkashin inuwar jam’iyya ba.
A ranar Litinin ne kuma kuma jam’iyyar NNPP ta koka kan rashin ba ta takardun kofin hukuncin kotun, tana mai cewa ya kamata a ba ta kofin takardun hukuncin domin lauyoyinta su nazarce su domin daukaka kara zuwa kotu koli.
A ranar Talata ne wasu takardu da ke nuna cewa daga kotun suke – wadanda ke dauke da kunshin hukuncin suka zo da wani abu na bazata.
Musamman a shafi na 67 na takardun hukuncin.
A shafin alkalin ya rubuta cewa “Kotu ta samu cewa dukkannin abubuwan da ake ayyanawa a kansu a cikin wannan shari’a ta bangaren wanda ake kara ne suka yi nasara a kansu”.
Mai kara a nan shi ne Abba Kabir Yusuf, yayin da APC da Nasiru Yusuf Gawuna suka kasance wandanda ake kara.
Kotun ta ƙara da cewa ”Saboda haka wanda ke kara shi ne wanda ya yi nasara a kan wanda ake kara”.