An gano gawarwaki 9 sakamakon wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a Neja – NSEMA

Boat mishap 750x430
Boat mishap 750x430

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce an gano gawarwaki tara a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Shugaban Hukumar Agaji da Gyaran Jama’a na NSEMA, Alhaji Salihu Garba ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna ranar Lahadi.

NAN ta tuna cewa an tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa da su, ‘yan kasuwa ne, suna jigilar kaya ne daga unguwar Zongoru da ke gundumar Bassa zuwa Gijiwa, gabanin kasuwar Juma’a da ke Kuta, hedikwatar karamar hukumar Shiroro, a lokacin da lamarin ya faru.

Akalla mutane 34 aka ce suna cikin jirgin wanda 10 daga cikinsu aka yi zargin sun rasa rayukansu.

Garba ya bayyana sunayen wadanda suka rasu sun hada da Farida Muntari, Sharhabila Sagir, Bubakar Sadiq, Na’ima Ibrahim, Amina, Safaratu Ibrahim, Sadiq Ibrahim da Rafiya Yakubu.

Ya ce har yanzu hukumar ba ta tantance biyu daga cikin mutanen da suka mutu ba, ya kara da cewa dukkan wadanda suka mutu ‘yan garin Zangoro ne.

Ya ci gaba da cewa, akwai maza da mata manya 24 da kuma yara maza da mata 10 a cikin jirgin a lokacin da ya kife.

Garba ya kuma ce ana ci gaba da bincike don gano sauran gawarwakin. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here