Hukumar NYSC Ta Musanta Rade-radin Tura Masu Bautar Kasa Nijar Don Taimaka Wa Sojoji

0
NYSC Caps
NYSC Caps

Hukumar Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa za ta tura masu bautar kasa zuwa Nijar don taimaka wa sojoji. Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Mista Eddy Megwa shi ya bayyana haka a ranar Asabar 5 ga watan Agusta a Abuja.

Sanarwar na zuwa ne bayan yada wani faifan bidiyo da aka yi a kafafen sada zumunta cewa za ta tura masu bautar kasa zuwa Nijar don yin yaki.

Ya ce: “Hukumar NYSC na sanar da ku cewa babu kanshin gaskiya a bidiyon da wani mai barkwanci ke yadawa.”

“Mutane da matasa masu bautar kasa da iyalansu duk su yi watsi da wannan labari da ke dauke da karairayi.

“Duk wasu masu barkwanci an shawarce su da su guji yada jita-jita da ke kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.” Megwa ya ce hukumar za ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta kamo wadanda suka yada wannan labari don su girbi abinda su ka shuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here