Kotun daukaka kara da ke zaman ta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar Alhamis 23 ga watan nuwambar da muke ciki na shekarar 2023, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Nasarawa.
Idan za a iya tunawa Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ne ya shigar da kara gabanta yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe, wanda ya sauke shi tare da ayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
A baya dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana da Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lash zaben gwamnan jihar, sai dai Ombugadu ya garzaya kotu yana kalubalanatar nasararsa.
A cewar hukumar ta INEC Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’u dubu 347,209, yayin da Ombugadu kuma ya yi rashin nasara da kuri’u dubu 283,016.
Sai a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar da muke ciki ta 2023 bayan da kotun ta zauna ta yanke hukunci inda ta ayyana Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.










































